Bishop na Cocin Katolika na Yola, Stephen Dami Mamza, ya taya al’ummar Musulmi murnar karamar Sallah wato Eid al-Fitr, inda ya buƙaci a ƙara himma wajen zaman lafiya da tausayi da kuma haɗin kai.
A saƙonsa na barka da Sallah ya taya Musulmi murnar kammala ibadar Azumi, tare da bayyana cewa Sallah tana tunatar da muhimmancin imani, sadaukarwa da taimakon juna.
Bishop din ya kuma mai da hankali kan halin da ake ciki a Arewa maso Gabas, a sakon nasa inda ya bayyana damuwa kan matsalolin tsaro da wahalhalu da al’umma ke fuskanta.
Har ila yau, ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su rike addu’a da haɗin kai da kaunar juna.
Bishop Mamza ya jaddada bukatar ƙarfafa zumunci tsakanin Musulmi da Kiristoci domin samar da zaman lafiya, da adalci da ci gaba mai ɗorewa.