Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kai hari kan shingen wasu jami’an soji a karamar hukumar Kukawa da ke jihar Borno tare da kashe wani kwamandan rundunar.
Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne yau Litinin da misalin karfe 12:30 na dare, inda suka ce maharan sun fito ne daga yankunan daban daban dake da alaqa da mashigar garin, tare da kai muggan hare-hare kan shingen sojojin.
Ko da yake su ma majiyoyi daga jami’an tsaro sun tabbatar da kai hari kan matsugunin jami’an tare da banka wa ababen hawan su wuta, wannan lamarin ya janyo mutuwar kwamnadan tawagar nan take.
Idan za’a iya tuna wa makamancin hakan ya faru kan jamian soji, inda ‘yan Boko Haram din suka kai wa sojojin harin, sai dai nan take jami’an suka mayar da martani.