Rundunar haɗin gwiwar sojin Iran ta Khatam al-Anbiya ta bayyana cewa ta yi amfani da sabon tsarin kariyar sararin sama a ranar Juma’a wajen harbo jirgin yaƙin Amurka.
Wani mai magana da yawun rundunar ya ce Iran za ta tabbatar da cikakken iko a sararin samaniyarta, bayan fiye da wata guda na mamayar jiragen saman Amurka da Isra’ila a lokacin yakin.
Kafin a harbe jirgin yakin na Amurka, Trump da sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth sun yi ikirarin cewa sun samu cikakken iko da sararin saman Iran.