Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce rundunar sojin Iran ta shirya don zuwan dakarun Amurka.
A wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na IRNA ya wallafa, Ghalibaf ya soki Trump saboda nuna sha’awar tattaunawa da Iran a fili, yayin da a ɓoye yake shirin kai farmaki ta ƙasa.
“Ina ganin abokin gaba a fili yana magana kan tattaunawa, amma a ɓoye yana shirin kai farmaki ta ƙasa. Mutanenmu suna jiran zuwan sojojin Amurka a ƙasa don buɗe musu wuta,” in ji shi.
Kafofin labarai na Amurka sun ruwaito cewa Pentagon na shirin ƙaddamar da ayyukan soji ta ƙasa a Iran na tsawon makonni, bayan rundunar sojin Amurka ta sanar da isowar sojoji 3,500 zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.