Fadar Shugaban Ƙasa ta ce dalilin da ya sa Bola Ahmed Tinubu ya gana da waɗanda harin Filato ya shafa a filin jirgin saman Jos shi ne rashin samun damar saukan jiragen sama da dare a filin jirgin.
Ta bayyana cewa wannan matsala ce ta lantarki, wanda ya sa aka zaɓi a yi ganawar a kusa da filin jirgi domin kauce wa matsalar tafiya cikin dare.
Lamarin dai ya biyo bayan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a jihar Filato, yayin da wasu ‘yan siyasa suka soki yadda aka gudanar da ziyarar a filin jirgi maimakon shigowa cikin gari domin ganewa idon sa halin da ake ciki.