Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Sanata Mpigi Barinada ya rasu
DSS za ta gurfanar da El-Rufai kan zargin laifukan yanar gizo da barazana ga tsaron Kasa
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kisan mutane 33 a jihar Kebbi

DSS za ta gurfanar da El-Rufai kan zargin laifukan yanar gizo da barazana ga tsaron Kasa

Shari’ar El-Rufai kan zargin Kutse da tsaron Kasa

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sanar da cewa za ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar 25 ga Fabrairu kan zargin aikata laifukan yanar gizo da kuma karya dokokin tsaron kasa.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta kotun tarayya da ke Abuja ce ta sanya ranar, bayan Babban alkalin kotun, Mai shari’a John Tsoho, ya mika mata shari’ar domin sauraro.

A baya, NAN ta ruwaito cewa DSS ta shigar da kara mai kunshe da tuhume-tuhume uku a ranar Litinin, inda ake zargin El-Rufai da hannu wajen satar bayanan wayar Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu.

A takardun kotu, an ce El-Rufai ya amince yayin wata hira da ya yi a shirin Prime Time na Arise TV a Abuja a ranar 13 ga Fabrairu cewa shi da wasu abokan aikinsa sun yi kutse cikin sadarwar wayar NSA.

Masu gabatar da kara sun bayyana cewa laifin ya saba da Sashe na 12(1) na Dokar Laifukan Yanar Gizo ta 2024, wadda ta tanadi hukunci kan irin wannan laifi.

A tuhuma ta biyu, an ce tsohon gwamnan ya bayyana a hirar cewa ya san wani mutum da ya yi kutse cikin sadarwar NSA amma bai kai rahoto ga hukumomin tsaro ba.

Ana sa ran za a fara sauraron shari’ar a ranar 25 ga Fabrairu a gaban Mai shari’a Abdulmalik a Abuja.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use