Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

EFCC ta tsawaita tsare El-Rufai

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFFC a Najeriya ta tsawaita zaman tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a hannunta a ranar Talata.

El-Rufai ya shafe dare na biyu a hannun hukumar yayin da lauyansa, A.U Mustapha (SAN), ke neman a bada beli.

Duk da haka, akwai alamun cewa hukumar na iya neman damar daga kotu ta ci gaba da tsare shi don amsa tambayoyin hukumar ta EFCC

Tsohon gwamnan ya kai kansa hedikwatar EFCC da ke Abuja a ranar Litinin da misalin karfe 10 na safe domin yi masa tambayoyi dangane da zargin binciken cin hanci da rashawa na naira biliyan 432.

Duk da haka, an tsare shi a hukumar, inda masu bincike suka ci gaba da yi masa tambayoyi.

Wani jami’in hukumar da ya nemi a boye sunansa ya ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa tana yunkurin samun izinin tsare shi bayan sa’o’i da doka ta bada a tsare shi ya kare.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use