Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Eid Al Fitr: Malamin addini ya saɓa umarnin Sarkin Musulmi a Sokoto

Sheikh Musa Lukuwa yayin da ya jagoranci mabiyansa sallar Eidi-al-Fitr a masallacinsa da ke Mabera, Sokoto, ranar Alhamis

Wani malamin addinin Musulunci a Jihar Sokoto Sheikh Musa Lukuwa ya jagoranci sallar Idi tare da mabiyansa duk da umarnin Sarkin Musulmi na jinkirta Sallah, sakamakon rashin ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa malamin ya dogara ne da bayanan ganin wata daga Jamhuriyar Nijar, wanda ya tabbatar masa da shigowar watan Shawwal, shi ya sa ya yanke shawarar gudanar da sallar Idi.

Wannan mataki ya haifar da cece-kuce a tsakanin al’umma, inda wasu ke ganin ya yi daidai bisa hujjar addini, yayin da wasu ke sukar matakin tare da cewa ya saɓa wa umarnin shugabancin addini, wanda ya kamata a bi domin tabbatar da haɗin kai da kauce wa rikice-rikice.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use