Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Farashin litar man fetur ya kai N1,200 a Ibadan

Farashin man fetur ya ƙaru zuwa kusan ₦1,080 a kowanne lita a wasu sassan Lagos, yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ya ɗaga farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

Bincike a wasu gidajen mai a Legas a ranar Asabar ya nuna cewa farashin litar man fetur, yanzu yana tsakanin ₦1,020 zuwa ₦1,080 gwargwadon wuri da kuma gidan man.

Ƙarin ya biyo bayan karin farashin litar man fetur ne da matatar man Dangote ta yi daga Naira N875 zuwa 995 zuwa sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Masana makamashi sun bayyana cewa rikicin da ke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran na iya ƙara matsa kasuwar man fetur ta duniya, wanda zai iya haifar da karin farashi a Najeriya.

Haka kuma, rahotanni daga Ibadan sun nuna cewa farashin litar man fetur din ya kai ₦1,200 a a wasu gidajen mai.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use