Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Tumatir ba zai kara kudi ba a lokacin Ramadan – Manoma

Tumatir ba zai yi tsada ba a Ramadan kamar yadda manoma suka yi hasashe (Hoto/Unsplash/Engin Akyurt)

Kungiyar manoma, masu sarrafawa da kuma ’yan kasuwar tumatir ta Najeriya (TOMAPMAN) ta fada cewa a bana farashin tumatir da sauran kayan lambu ba zai karu ba kamar yadda aka saba gani a duk lokacin Ramadan.

Shugaban kungiyar a jihar Kaduna, Malam Rabiu Zuntu, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar lahadi a jihar Lagos.

Zuntu ya ce, ana sa ran farashin kayan lambu zai kara sauka a lokacin Ramadan sabanin shekarun baya, saboda yawaitar noma da kuma raguwar bukata.

Ya kara da cewa azumin Ramadan na bana, wanda zai fara a watan Fabrairu ya kuma kare a Maris, ya zo ne daidai lokacin kololuwar girbin tumatiri.

Har ila yau, Zuntu ya bayyana cewa a halin yanzu, kwandon tumatir mai nauyin kilo 50 na bai wuce tsakanin Naira 7,000 zuwa Naira 10,000 a kasuwannin Arewacin Najeriya.

Ya kuma jaddada cewa ’yan Najeriya kar su yi fargaban karin farashi a lokacin Ramadan sakamakon yawan tumatir da kuma karancin bukatarsa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use