Shahararren malamin addinin Musulunci a Zariyar Jihar Kaduna, Sheikh Usman Idris Kusfa, wanda aka fi sani da ‘Rigi-Rigi,’ ya rasu yana da shekara 57.
Wani babban almajirin malamin, Nasiruddeen Umar, wanda aka fi sani da Baharu ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a ranar Litinin a Zariya.
Umar ya ce Sheikh Kusfa ya rasu da sanyin safiyar Litinin a wani asibiti mai zaman kansa da ke Kaduna bayan ya yi fama da rashin lafiya na tsawon watanni.
A cewarsa, Kusfa ya shahara sosai da koyarwar addinin Musulunci kuma ya samu karbuwa sosai a TikTok da sauran shafukan sada zumunta.
Ya ce malamin ya rasu ya bar mata hudu, ‘ya’ya 37, da jikoki da yawa.
Umar ya kara da cewa an shirya yin jana’izar marigayin a Kusfa, birnin Zariya, da karfe 4:30 na yamma a ranar Litinin.