Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

G20 ta kammala taro ba tare da Amurka ba

An gudanar da taron G20 na bana ne a 2025 (Hoto: Getty)

An kammala taron ƙungiyar G20 a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu, inda shugabannin ƙasashen da ke da ƙarfin tattalin arziki suka tattauna batutuwan da suka shafi duniya.

Shugaban ƙasar mai masaukin baki, Cyril Ramaphosa, ya ce mahalarta taron sun jaddada muhimmancin aiki tare domin fuskantar manyan kalubale.

Ƙungiyar ta cimma matsaya kan ɗaukar matakai a kan sauyin yanayi, duk da cewa Amurka ta ƙi halarta.

Fadar White House ta ce gwamnatin Afirka ta Kudu ta karkatar da shugabancin G20 zuwa abin da ta kira “makamin yaƙi”, tana mai cewa Amurka za ta gyara wannan a shekara mai zuwa, lokacin da za ta karɓi shugabancin ƙungiyar.

Amurka ta ƙaurace wa taron ne bayan da Shugaba Donald Trump ya yi zargin da ake kallo “mara tushe” cewa gwamnati a Afirka ta Kudu na zaluntar ƴan tsirarun fararen fata.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use