Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Gawuna ya yi murabus daga shugaban kwamitin gudanarwa na Mortgage Bank

Gawuna Gawuna
Ana sa ran zai fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC ranar Talata (Abubakar Musa DK)

Nasiru Yusuf Gawuna ya yi murabus daga shugaban kwamitin gudanarwa na bankin bayar da rancen sayen gida, wato Mortgage Bank.

Rahotanni sun nuna cewa matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake zargin yana shirin sauya sheƙa a harkokin siyasa.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Gawuna ya kammala tattaunawa da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Ana sa ran zai fice daga jam’iyyarsa tare da komawa jam’iyyar ADC a ranar Talata.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun masu sauya sheƙa a siyasar jihar Kano da ma kasa baki ɗaya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use