Gwamnatin Ghana ta ce za ta buɗe iyakokinta ga dukkan ‘yan Afirka domin shiga ƙasar ba tare da biza ba daga 25 ga watan Mayu, 2026.
Shugaban ƙasar, John Dramani Mahama, ya ce wannan mataki zai ƙarfafa dangantaka da zumunci tsakanin ƙasashen nahiyar, yana mai jaddada muhimmancin sauƙaƙa zirga-zirga a tsakanin Afirka.
Sabuwar manufar ta ba kowane ɗan Afirka damar ziyartar Ghana cikin sauƙi don kasuwanci, ziyara, ko karatu, ba tare da wahalar neman biza ko biyan kuɗi ba.
Za a yi amfani da wani dandalin intanet na musamman domin neman izinin shiga ƙasar kyauta, wanda zai rage ɓata lokaci da tsadar tafiye-tafiye a tsakanin ƙasashen Afirka.
Ghana ta bi sahun ƙasashen da suka riga suka buɗe iyakokinsu, kamar Rwanda da Gambia, sai dai gwamnati ta tabbatar da cewa za a tsaurara matakan tsaro a iyakoki don tabbatar da zaman lafiya.