Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Gwamna Zulum ya rushe majalisar zartarwar jihar Borno

Zulum Zulum
An umarci dukkan kwamishinoni su mika ragamar ma’aikatunsu (Gwamnatin Borno)

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da rusa Majalisar Zartarwar jihar nan take.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin bai wa duk wani jami’in gwamnati da ke da sha’awar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa damar yin hakan cikin sauƙi.

Gwamnan ya kuma umarci dukkan kwamishinoni da su mika ragamar ma’aikatunsu ga sakatarorin dindindin kafin ranar Juma’a, 3 ga Afrilu, 2026.

Zulum ya gode wa tsofaffin kwamishinonin bisa gudummawar da suka bayar, jajircewa da kuma irin ayyukan ci gaba da suka gudanar domin al’ummar jihar Borno.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use