Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Gwamnan Adamawa Fintiri ya sauya sheƙa zuwa APC

Gwamnan jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, Ahmadu Fintiri ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Sauya shekar da gwamnan yayi na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 48 da komawar Kakakin majalisar dokokin jihar Bathiya Wesley APC daga PDP tare da wasu ‘yan majalisar jihar.

A safiyar wannan rana ta Juma’a ce dai gwamnan ya yanki katin jam’iyar a mazabar K/Wuro Ngayandi da ke karamar hukumar Madagali a jihar ta Adamawa, lamarin da ya tabbatar da komawarsa jam’iyyar ta APC mai mulki.

A jawabin da gwamnan ya yi sa’ilin da yake yankar katin jam’iyyar, ya ce ya bar tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP ne biyo bayan tuntuɓa da shawarwari daga kwararru, wanda acewar sa, hakan da ya yi, zai kawo ci gaba mai ɗorewa ga jihar.

Kazalika, Fintiri ya ƙara da cewa, hakan da yayi zai taimaka wajen cika muradun shugaban ƙasa Bola Tinubu na samar da walwala da ayyukan ci gaba haɗi da haɓaka tattalin arzikin ƙasa.

Rahotanni sun bayyana cewa, kafin ficewarsa daga PDP, gwamnan ya yi ganawa daban-daban da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta APC.

Ko a ranar Larabar da ta gabata ma, mataimakin shugaban jam’iyyar APC shiyyar Arewa maso gabas, Mustapha Salihu, ya jagoranci wata tawaga ta musamman don ganawa da gwamnan a gidan gwamnatin jihar, da ke birnin Yola.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use