Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya nuna alamun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa ADC, inda ake sa ran zai bayyana matsayinsa a hukumance ranar Alhamis.
Gwamnan, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin wata tawagar ADC karkashin jagorancin Babachir Lawal a gidan gwamnati da ke Bauchi.
Jaridar Punch ta ruwaito Bala Mohammed ya danganta wannan mataki da rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP, yana mai cewa duk kokarin sulhu da aka yi bai yi nasara ba.