Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a ranar Juma’a, ya bai wa Limamai 40 na masallatan Juma’a a fadin jihar motoci domin tallafa musu wajen gudanar da ayyukansu na addini yadda ya kamata.
Yayin da yake jawabi a wajen miƙa motocin, gwamnan ya ce an yi wannan tallafin ne domin inganta zirga-zirgar limaman, ta yadda za su ƙara faɗaɗa wa’azinsu da kuma hulɗa da al’umma.
Ya bayyana cewa Jihar Zamfara tana da tushe mai karfi a kan koyarwar addinin Musulunci, inda limamai ke yi wa al’umma hidima a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar. Ya ƙara da cewa jin daɗin shugabannin addini na daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.
A cewarsa, limamai 40 da suka ci gajiyar motocin su ne rukunin farko na wannan shiri, wanda za a ci gaba da aiwatar da shi nan gaba.
“Muna kan gina masallatai da gidaje wa limamai, kuma muna ganin yana da muhimmanci su riƙa zirga-zirga cikin sauki,” in ji shi.