Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Alhamis 19 da kuma Juma’a 20 ga watan Maris a matsayin hutu don shagulgulan bikin Sallah.
Wata sanarwa da ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya fitar, ya taya al’ummar Musulmi murna tare da fatan yin bukukuwa lafiya.
Ya bukaci Musulmi da su dabbaka zaman lafiya, kauna da kuma sadaukarwa da suka koya lokacin azumi.