Gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin rufe wurin hakar ma’adinai nan take a Jihar Plateau bayan da aka ruwaito cewa kimanin mazauna ƙauyen Zurak 37 sun mutu sakamakon shaƙar iskar gas mai guba yayin ayyukan hakar ma’adinai.
Wani mai sharhi kan tsaro Zagazola Makama ya wallafa a shafin sa na X cewa an kwantar da wasu mutane 25 a asibiti bayan sun shaƙu da hayakin carbon monoxide a wurin hakar ma’adinai da ke Zurak, wanda ke cikin ƙaramar hukumar Wase.
A cewar rahoton, waɗanda abin ya shafa, galibinsu samari ne ‘yan shekara 20 zuwa 35, suna gudanar da ayyukan hakar ma’adinai na ƙarƙashin ƙasa na yau da kullun lokacin da suka shaƙi iskar gas mai guba da ake kyautata zaton ta taru a cikin ramukan da ba su da iskar shaƙa ba.
Bayan lamarin, Ministan kula da ci gaban Ma’adanai, Dele Alake, ya ba da umarnin a dakatar da duk wani aiki a cikin Lasisin Haƙar Ma’adinai mai lamba 11810, wanda Solid Unit Nigeria Limited ke gudanarwa, bayan iftila’in da ya faru a yankin Zurak na ƙaramar hukumar Wase.
Ministan ya ba da umarnin a cikin wata sanarwa da Mataimakin sa na musamman kan kafafen yaɗa labarai, Segun Tomori, ya fitar a ranar Laraba a Abuja.