Gwamnatin Najeriya ta nuna fargaba kan ƙaruwar tashin hankali a ƙasashen yankin Gulf wanda ta ce zai iya haifar da mummunan tasiri ga zaman lafiyar yankin da ma duniya baki ɗaya.
Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar, ta yi kiran kai zuciya nesa da kuma buƙatar dukkan ɓangarori su kwantar da hankali da kauce wa duk wani yunkuri da zai jawo bazuwar rikicin.
“Najeriya na kira na ganin an rage amfani da ƙarfi don kare rayukan fararen hula da kauce wa duk abin da zai iya saɓa wa dokokin duniya,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta kuma bayyana muhimmancin amfani da tattaunawar dfilomasiyya don samar da masalaha maimakon shiga yaƙi da juna.