Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Gwamnatin tarayya ta bai wa ‘yan kasuwar Singa tallafin naira biliyan biyar

Gwamnatin tarayya ta bai wa ‘yan kasuwar Singa da gobara ta shafa tallafin naira biliyan biyar.

Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan yayi ziyarar jaje da ya kai kasuwar a yau Litinin.

Hakan na zuwa ne bayan wata mummunar gobara da ta auku a kasuwar sayar da kayan masarufi ta Singa a yammacin Asabar.

A baya-baya nan dai ana samun yawaitar afkuwar gobara a kasuwannin jihar Kano, wanda ake danganta wa da matsalar lantarki.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use