Kungiyar Gwamnonin Najeriya, NGF, ta bayyana hare-haren kunar bakin-wake da aka kai a Maiduguri a daren Litinin a matsayin abin takaici da kuma kyama.
Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata ta hannun shugabanta, gwamna Abdulrahaman Abdulrazaq, ta ce abubuwan da suka faru sun kasance barnatar da rayukan mutane ba tare da wani dalili ba.
Kungiyar ta bukaci hukumomin tsaro da su dakile barazanar ‘yan ta’adda wajen kai irin wadannan hare-hare.
Ta kuma yi Alla-wadai da hare-haren da aka kai tare da tabbatar wa jami’an tsaro ci gaba da goyon bayan ayyukan da za su kawo karshen wannan matsala.