Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Hare-hare kan cibiyoyin makamashi sun sauya salon yaki a Gabas ta tsakiya

Qatar ta kai ƙorafi ga MDD kan hare haren Iran Qatar ta kai ƙorafi ga MDD kan hare haren Iran
Qatar ta kai ƙorafi ga MDD kan hare haren Iran

Rikicin da ke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ya ɗauki sabon salo mai haɗari, bayan da aka fara kai hare-hare kan manyan cibiyoyin makamashi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Lamarin ya ƙara ɗaukar hankali ne bayan harin da Isra’ila ta kai kan babban filin gas na Kudancin Pars, wanda ke ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan tattalin arzikin Iran.

Wannan hari ya nuna sauyi daga kai farmaki kan sojoji zuwa lalata muhimman cibiyoyin tattalin arziki.

A martanin da ta mayar, Iran ta kai hare-hare kan wasu cibiyoyin makamashi a ƙasashen Qatar, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, lamarin da ke nuna faɗaɗar rikicin zuwa yankin Gulf baki ɗaya.

Wani masani kan harkokin tsaro da siyasar ƙasa da ƙasa, Hamidreza Azizi, ya bayyana cewa wannan sabon salo na hare-hare yana nuna gagarumin sauyi a yadda yaƙin ke gudana.

A cewarsa, harin Isra’ila ya nuna cewa yanzu ana kai hari ne kai tsaye kan ginshiƙan tattalin arziki, ba wai kawai kan rundunonin soji ba.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use