Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya bayyana cewa hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da ƙasarsa ke kai wa Iran za su ƙaru sosai a wannan makon.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taro da jami’an soji.
A cewar jaridar The Times of Israel, Katz ya ce: “Isra’ila ta kuduri aniyar ci gaba da jagorantar hare-haren kan gwamnatin Iran, domin raunana shugabanninta da kuma dakile ƙarfinta na dabarun soja, har sai an kawar da duk wata barazana ga tsaron Isra’ila da kuma muradun Amurka a yankin.”
Ministan ya kara da cewa “ba za mu tsaya ba har sai an cim ma dukkan muradun yaƙin.”