Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana a ranar Asabar cewa Iran ta nemi afuwar ƙasashe makwabta a Gabas ta Tsakiya, kuma ta yi alkawarin dakatar da kai musu hare-hare saboda matsin lambar sojojin Amurka da Isra’ila.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth, Trump ya ce Iran ta yi wannan alkawari ne “saboda hare‑haren da Amurka da Isra’ila ke kai mata ba dare ba rana.”
Trump ya ce Iran ta yi ƙoƙarin mamaye yankin Gabas ta Tsakiya, amma daga baya ta sha ƙasa.
Shugaban na Amurka ya kuma yi ikirarin cewa wannan shi ne karon farko cikin dubban shekaru da Iran ta sha kashi daga makwabtanta a yankin, inda ya ce wasu daga cikin ƙasashen sun gode masa. “Sun ce, ‘Mun gode, Shugaba Trump.’ Ni kuma na ce, ‘Ba damuwa!” in ji shi
Trump ya ƙara da cewa Iran ba za ta iya ci gaba da cin zarafin makwabtanta ba, sannan ya yi gargaɗin cewa za a ci gaba da kai munanan hare-hare a kan kasar saboda “mummunan hali” da ayyukanta.
A safiyar Asabar ɗinnan ne dai Shugaban ƙasar iran Masoud Pezeshkian, ya ce ba za su ci gaba da kai hari kan kasashe makwabta ba, sai dai idan daga maƙwabtan aka kai wa kasarsa hari