Aƙalla mutum 180 ne suka jikkata sakamakon hare-haren makamai masu linzami na Iran da suka afka garuruwan Arad da Dimona a kudancin Isra’ila, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta ƙasar.
Dimona wadda ke ɗauke da babbar cibiyar nukiliyar Isra’ila da kuma Arad da ke kusa, Iran ta ce ta kai masu hare-haren makamai masu linzami ne a matsayin ramuwar gayya bisa harin da aka kai cibiyar Natanz a ƙasar.
Sabbin alkaluman da Ma’aikatar Lafiya ta Isra’ila ta fitar sun nuna cewa mutum 116 sun jikkata a Arad, ciki har da bakwai da ke cikin mawuyacin hali, yayin da a Dimona kuma mutum 64 suka jikkata, ciki har da guda ɗaya mai mummunan rauni.
Harin ya yi barna mai yawa, inda makamai biyu da suka bugi wuraren kai tsaye suka lalata gaban gine-ginen zama tare da haƙa manyan ramuka a ƙasa.
Tsarin kariyar sararin samaniya na Isra’ila ya gaza dakile makaman duk da an harba masu tarewa, lamarin da ya sa rundunar sojin Isra’ila bayyana cewa za ta binciki abin da ya faru domin gano dalilin gazawar.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana lamarin a matsayin “maraice mai matuƙar wahala”, yana mai cewa Isra’ila za ta ci gaba da kai hare-hare kan Iran.