Mutane tara ne aka tabbatar sun mutu bayan wani makami mai linzami na Iran ya fada kan wani gini kusa da birnin Kudus a ranar Lahadi da rana.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Isra’ila ta ce makamin ya yi karo kai tsaye da wani gini a birnin Beit Shemesh, lamari mafi muni tun bayan da Iran ta fara mayar da martani da harba makamai masu linzami sakamakon hare-haren hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila a ranar Asabar.
Hukumar agajin gaggawa ta kasa, wadda ake kira Magen David Adom, ta ce kusan mutane 30 sun jikkata a harin, ciki har da mutum biyu da ke cikin mawuyacin hali.
‘Yan sandan Isra’ila sun bayyana a wata sanarwa cewa, “Sakamakon bugun kai tsaye da makamin ya yi, ginin ya samu mummunar barna har ma ya rushe wani bangare.”
Duk da cewa Isra’ila ta ce ta samu nasarar tare mafi yawan makaman da Iran ta harba tun bayan tashin hankalin, rundunar sojin kasar ta yi gargadin cewa tsarin kariyar sararin samaniyarta ba zai iya bada tabbacin kakkabe kowane makami ba.