Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama manajan wani otal tare da matasa 21 a yankin Kureken Sani, karamar hukumar Kumbotso.
An kama mutanen ne bisa zargin aikata ayyukan da suka saba ka’idojin addini da al’ada, a cewar hukumar.
Hisbah ta ce an gudanar da samamen ne bayan samun bayanan sirri, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin domin daukar matakan da suka dace.