Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Hukumomi sun san masu ɗaukar nauyin Boko Haram — Buratai

Tukur Yusuf Burutai (Tsohon Hafsan Sojin Najeriya)

Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Tukur Buratai, ya ce bai kamata a ɗora masa alhakin rashin bayyana sunayen mutanen da ake zargin suna ɗaukar nauyin ta’addanci a ƙasar ba.

Sai dai ya ƙara da cewa waɗanda ke ɗaukar nauyin ta’addancin sanannu ne, kuma suna cikin al’umma.

A wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma’a, tsohon hafsan sojan ya bayyana cewa hukumomin da abin ya shafa sun san waɗanda ke samar da kuɗaɗen, amma suna da dalilan da suka sa ba su bayyana sunayensu ba ga jama’a.

Ya ce: “Ba wai kawai ambaton sunaye ba ne; hukumomin nan sun san dalilin da ya sa ba a bayyana sunayen ba. Ya kamata a ɗauki mataki; waɗannan mutanen har yanzu suna cikin al’umma, kuma an san su.”

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use