Mohammed Bello El-Rufai, ɗan majalisar wakilai da ke wakilatar Kaduna ta Arewa, ya zargi ICPC da ɓata sunan mahaifinsa, Nasir El-Rufai ta hanyar amfani da shirun sa a matsayin makami a kansa.
Wata sanarwa da ya fitar a madadin iyalansu, ya ce abin takaici ne yadda hukumar ICPC ke gudanar da farfaganda a kafafen yaɗa labarai maimakon bin doka da tsari wurin gudanar da aikin ta.
Ya ƙara da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya bai wa kowane ɗan ƙasa haƙƙin yin shiru, kuma amfani da shi ba hujjar laifi ko rashin haɗin kai ba ne.
Iyalan sun kuma yi zargin cewa binciken ya samo asali ne daga takardar sammacin bincike ta bogi wadda wani alƙalin majistare ya bayar ba tare da hurumin babbar kotun tarayya ba.
Har yanzu ICPC ba ta mayar da martani kan zarge-zargen ba.