Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

ICPC ta ƙwato na’urar sauraron sirri a gidan El-Rufai

Hukumar ta zargi El-Rufai da ƙin ba da haɗin kai ga masu bincike

Hukumar ICPC ta ce ta ƙwato wasu na’urorin sa ido da ake zargin suna iya sauraron tattaunawar sirri da kuma samun takardun tsaro a gidan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ke Abuja.

A cewar takardun kotu, an ƙwato kayayyakin ne a lokacin bincike a idon matarsa, Hadiza El-Rufai da kuma ɗansa, Mohammed Bello.

Hukumar ta zargi El-Rufai da ƙin ba da haɗin kai ga masu bincike har sai an gurfanar da shi, tare da cewa ɗaya daga cikin mataimakansa ya tsere daga Najeriya.

ICPC ta bayyana hakan ne a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda tsohon gwamnan ke ƙalubalantar tsare shi da aka yi da kuma zargin take haƙƙinsa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use