Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Ina jin daɗin taka leda a Al-Nassr – Ronaldo

Ronaldo Ronaldo
Ronaldo ya koma Saudiyya ne a watan Disambar 2022

Cristiano Ronaldo ya ce yana jin daɗin taka leda a ƙungiyar Al-Nassr duk da raɗe-raɗin da ake yi kan makomarsa a ƙungiyar ta Saudiyya.

An ruwaito cewa ɗan wasan mai shekaru 41 ɗan ƙasar Portugal bai gamsu da yadda Asusun Zuba Jari na Saudiyya (PIF) ke tafiyar da ƙungiyar ba, kuma bai yi buga wasanni uku ba a baya-bayan nan.

Sai dai ya koma taka leda a makon jiya, kuma ya zura kwallo biyu a 4-0 da suka yi a kan Al-Hazem ranar Asabar — hakan ya sa suka koma na ɗaya a kan teburin gasar Saudiyya.

“Ina cikin farin ciki,” in ji ɗan wasan Portugal a wata hira da kafar yaɗa labarai ta Saudiyya Thmanyah. ““Ƙasar ta karɓe ni hannu bibiyu, tare da iyalaina da abokaina. Ina son ci gaba da zama a nan.

Ronaldo ya koma Saudiyya da wasa a watan Disambar 2022 bayan cimma matsaya don kawo karshen kwantiraginsa a Manchester United, inda ya zama ɗan wasa mafi tsada da zai karɓi albashi mai tsoka a tarihin kwallon kafa kan fam miliyan 177.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use