Hukumar zaɓe ta kasa INEC na fuskantar matsin lamba daga jam’iyyun adawa sakamakon rikicin shugabanci da ya addabi jam’iyyar ADC, gabanin zaɓen 2027.
Jam’iyyar ADC ta zargi INEC da nuna son kai da kuma ƙoƙarin raunana ƴan adawa, yayin da ita kuma hukumar ta ce matakan da ta ɗauka sun biyo bayan umarnin kotu ne kuma tana aiki ne bisa doka.
A gefe guda, jam’iyyar APC ta yi watsi da zarge-zargen, tana mai cewa matsalolin ADC na cikin gida ne ba wai sakamakon wani tsoma baki ba.
Lamarin na ƙara ɗaukar zafi yayin da ake ganin rikicin ADC da cece-kuce kan INEC na iya tasiri ga siyasar Najeriya kafin zaɓen 2027.