Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

INEC ta ce ta yi rajistar sabbin masu zabe sama da miliyan uku

INEC ta ce matasa sun fin yawa a sabbin rajistar zabe da ta yi INEC ta ce matasa sun fin yawa a sabbin rajistar zabe da ta yi
Matasa ne suka fi yawa a sabbin masu rajistar zabe yayin da INEC ke ci gaba da aikin CVR a fadin Najeriya.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa mutane miliyan 3.44 sun kammala rajistar zabe a zagaye na biyu na shirin yin rajista zuwa ranar 3 ga Afrilu.

Rahoton da hukumar ta fitar ya nuna cewa an samu karin masu rajista daga sassa daban-daban na Najeriya, ta hanyar rajista ta intanet da kuma ta kai-tsaye.

Daga cikin adadin, sama da mutane miliyan 2 sun kammala rajistar su ta intanetyayin da kusan miliyan 1.37 suka yi rajista a cibiyoyin yin rajista.

A bangaren jihohi, Jigawa ce ke kan gaba wajen yawan wadanda suka yi rajista, sai Legas na biyu, yayin da Kano ke matsayi na uku a jerin.

Rahoton ya kuma nuna cewa matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 su ne kan gaba wajen rajista, inda suka kai fiye da kashi 68 cikin 100 na sabbin masu rajistar zabe.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use