Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Iran ta ce kafofin watsa labaran Amurka na sauya mata magana

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa kafofin watsa labaran Amurka suna sauya magana da matsayar Iran.

Ministan ya jaddada cewa gwamnatin Iran na matuƙar godiya ga Pakistan kuma ba su taɓa ƙin ziyartar Islamabad ba.

Araghchi ya ce babban burin Iran shi ne samun sharuddan da za su kawo ƙarshen haramtaccen yaƙin da aka kakaba wa ƙasar a yanzu.

A wani rubutu da ya yi a shafin X, ya bayyana cewa “Abin da muka mai da hankali a kai shi ne cikakkun sharuddan kawo ƙarshen haramtaccen yaƙin da aka kakaba mana.”

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use