Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Iran ta ce ta katse zirga-zirgar jiragen Isra’ila da hare-haren jirage marasa matuƙa

Tehran ta ce ta yi nasarar katse zirga-zirgar jiragen sama da kuma ayyukan sanya mai na jiragen sojin Isra’ila, bayan kai hare-haren jirage marasa matuka kan tankunan mai da jiragen da ke sa mai a filin jirgin Ben Gurion kusa da Tel Aviv.

A cikin wata sanarwa, rundunar sojin Iran ta ce hare-haren da sojojinta da kuma dakarun rundunar juyin juya hali suka kai kan wuraren sojan, sun tilasta wa Isra’ila kwashe wasu daga cikin sojojinta daga wuraren.

Sanarwar ta ƙara da cewa hare-haren za su ci gaba da tsananta har sai an kawar da duk wata barazana da Iran ke fuskanta.

Filin jirgin Ben Gurion, wanda ke ‘yan kilomita kaɗan a kudu maso gabashin Tel Aviv, na ɗauke da wasu rukunin sojojin Isra’ila na musamman, kuma yana kusa da wuraren gyara da kula da jiragen yaƙin ƙasar ta Isra’ila.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use