Sakataren majalisar tsaron Iran, Ali Larijani ya ce a shirye ƙasar take don fafata yaƙi mai tsawo saɓanin Amurka.
Wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a yau Litinin, ya ce fiye da shekara 300 Iran ba ta taɓa tsokanar faɗa ba, kuma dakarun sojin ƙasar ba su taɓa shiga wani yaƙi ba sai na kare kai.
”Saboda haka duk abin da zai faru, za mu kare kan mu, kuma za mu yi amfani da kafuwar daularmu na tsawon shekara 6,000 don tabbatar da ganin maƙiya ba su samu nasara a kan mu ba,” in ji shi.
Isra’ila da Iran na ci gaba da far wa juna ta hanyar kai hare-hare, sai dai ana ta samun kiraye-kirayen cewa ya kamata ɓangarorin su tsagaita wuta tare da komawa teburin tattaunawa.