Wani babban jami’in kasar Iran, Ali Larijani, ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan yiwuwar lalata tsarin wutar lantarkin Iran.
Rahotanni sun bayyana cewa Trump ya taɓa cewa Amurka na da ikon rusa dukkan karfin wutar lantarkin Iran cikin awa guda, amma ba su yi hakan ba.
Sai dai Larijani ya yi gargadin cewa duk wani irin hari kan tsarin wutar lantarkin Iran zai iya janyo matsala mai girma ga yankin gabas ta tsakiya baki daya.
A cewarsa, idan Amurka ta dauki irin wannan mataki, yankuna da dama na Gabas ta tsakiya za su fada cikin duhu cikin ƙasa da rabin awa.
Ya kara da cewa wannan yanayi na duhu zai iya haifar da rikice-rikice da kuma barazana ga jami’an sojin Amurka da ke yankin.
Larijani ya jaddada cewa Iran na da karfin kare kanta, kuma duk wani mataki na farmaki daga Amurka zai iya haifar da martani mai tsauri da zai shafi tsaron yankin baki daya.