Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Iran ta harba makaman roka Isra’ila

Hoton wasu yankuna a Isra'ila

Iran ta harba makaman roka a wasu yankunan Isra’ila da ke da yawan jama’a da safiyar yau Asabar, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin.

Tuni ma’aikatan agajin gaggawa suka garzaya domin kai ɗauki a biranen Petah Tikva da Ramat Gan, inda aka samu rahotannin ɓarna da firgici.

A wani ɓangaren kuma, Bahrain ta umarci al’ummarta da su nemi mafaka bayan na’urorin gargadi sun yi ƙara a sassan ƙasar, sakamakon barazanar hare-hare.

Haka kuma, a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, wani wurin sarrafa iskar gas ya kama da wuta, bayan faduwar wasu tarkacen abubuwa da ake zargin sun faɗo daga sama.

A Kuwait ma, an samu rahotannin lalacewar wasu muhimman ababen more rayuwa, ciki har da tashoshin lantarki, matatar mai da kuma wuraren tace ruwan sha sakamakon hare-haren da aka kai.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use