Kamfanin dillancin labarai na Iran, Fars News, ya ruwaito wata majiya daga gwamnatin Iran na cewa babu wata tattaunawa da Iran ta yi da Donald Trump ta kai-tsaye ko kuma da masu shiga tsakani.
Majiyar ta kuma yi zargin cewa Trump “ya lashe amansa ne kawai” bayan an gargaɗe shi cewa Iran za ta kai hare-hare kan tashoshin wutar lantarki a yankin Tekun Fasha da kuma a Isra’ila.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar, ta ce kalaman Trump bata lokaci ne kawai, kuma yana yi don samun damar kara shiri na daukar matakin soji.
Sai dai, sanarwar ta kara da cewa akwai hobbasa da kasashen yankin ke yi na rage barazanar zaman fargaba da ake yi, amma Tehran ta ce duk abin da faru su tuhumi Amurka saboda ita ta fara yakin.

Hakan na zuwa ne bayan mista Trump ya yi ikirarin tatattaunawa da Iran din don ganin an kawo karshen yaki.