Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce ba za a ci gaba da kai hari kan ƙasashe makwabta ba, sai dai idan daga gare su aka kai wa ƙasarsa hari.
Ya bayyana cewa majalisar wucin gadi na shugabancin Iran ce ta amince da wannan matakin a ranar Juma’a.
Shugaban ya kuma nemi afuwar makwabtan ƙasashe kan hare-haren da ta kai musu kwanannan.
An kai hare-hare ƙasashen da ke yankin gabas ta tsakiya da suka hada da Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Kuwait da Bahrain saboda kasancewar kadarorin Amurka a cikinsu ko kusa da iyakokinsu.
A yankin na gabas ta tsakiya, hare-haren sun janyo mace-mace, lalacewar kadarori, tangarda a harkar sufurin jiragen sama, rufe sararin samaniya, da kuma mummunar illa kan samar da mai da iskar gas wanda ke shafar duniya baki ɗaya.
Ministan makamashi na Qatar, Saad al-Kaabi, ya ce idan yakin ya ci gaba, fitar da makamashi daga yankin zai iya tsayawa cik cikin ‘yan makonni, abin da zai haifar da hauhawar farashin makamashi, ƙarancin wasu kayayyaki, da tangarda a masana’antun a duniya.