Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Iran ta yi barazanar faɗaɗa yaƙi idan Amurka ta tsallake iyaka

Shirin ganawar Amurka da Iran a Pakistan ya janyo rudani kan halartar JD Vance Shirin ganawar Amurka da Iran a Pakistan ya janyo rudani kan halartar JD Vance
Tattaunawar Amurka da Iran a Pakistan na fuskantar cece-kuce kan halartar manyan jami’ai, ciki har da JD Vance.

Iran ta yi gargaɗi mai ƙarfi cewa za ta faɗaɗa yaƙi zuwa wajen yankin Gulf idan Amurka ta tsallake abin da ta kira “jan layi” a rikicin da ake ci gaba da yi.

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar IRGC ta ce idan aka ƙara tsananta hare-haren Amurka, za su kai farmaki kan muhimman cibiyoyin makamashi da ababen more rayuwa domin hana Amurka da ƙawayenta cin gajiyar man fetur da iskar gas na yankin na tsawon lokaci.

Wannan barazana na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke ƙara tsananta tsakanin Iran da Amurka, inda ake fargabar yaƙin na iya wuce iyakar Gabas ta Tsakiya zuwa wasu yankuna idan ba a dakatar da shi ba.

Masana da ƙasashe daban-daban sun nuna damuwa cewa ci gaba da wannan yanayi na iya jefa yankin cikin babbar matsala tare da barazana ga tsaron duniya baki ɗaya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use