Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Obi ya yi tir da kama malamin da ya gayyace shi zuwa Kaduna

Tsohon dan takarar shugaban kasa a tutar Labour a zaben shekarar 2023, Peter Obi, ya nuna damuwa kan wani malamin addini da aka kama, yana mai cewa hakan ta da zaune tsaye ne, da kuma kawo tasgaro ga dimokuradiyya.

Obi ya yi wannan jawabi ne a cikin wata sanarwa a shafinsa na X, inda ya ce ‘na samu sanarwar kama wani malamai a jihar Kaduna, mai suna sheikh Ahmad Tijjani Umar, bayan gayyatar da ya yi min zuwa jihar Kaduna ranar Lahadin da ta gabata’.

Tsohon gwamnan na Anambara, ya nuna damuwarsa kan wannan lamari, tare da bayyana hakan a matsayin cin zarafi ga ‘yancin malamin a matsayinsa na dan kasa, yana mai cewa wajibi ne ga wannan kasar ta ba wa kowa ‘yanci da dama ya yi magana kamar yanda dokar kasa ta bayar.

Obi ya ce irin wannan tauye hakkin da ake yi a Najeriya, shi ya kawo tasgaro ga demokuradiyya da cigaban kasar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use