Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Isra’ila da Amurka sun ƙaddamar da hare-hare kan Iran

Ƙasashen Isra’ila da Amurka sun ƙaddamar hare-hare a kan Iran a ranar asabar ɗinnan.

Kamfanin dillancin labaran Iran na Fars ya tabbatar da karar fashewa a babban birnin ƙasar Tehran da kuma biranen Qom da Kermanshah da Isfahan.

Hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da ake kokarin tattaunawa tsakanin jami’an Amurka da Iran don cimma yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran.

Firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu a jawabin da yayi bayan ƙaddamar da hare-haren haɗin gwiwar, ya ce sun yi hakan ne don kawar da barazana ga wanzuwar ƙasarsu.

Shi ma Shugaban Amurka Donald Trump a jawabin da ya gabatar bayan hare-haren, ya ce ƙasarsa ta gaji da batun yarjejeniyar nukiliyar Iran, inda ya sha alwashin wargaza makamanta masu linzami tare da lalata kamfanin ƙera makamanta da ke ƙarƙashin ƙasa.

Tuni dai Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya kan kasar Isra’ila da wasu sansanonin sojin Amurka da ke wasu daga cikin kasashen gabas ta tsakiya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use