Ministan Makamashi na Isra’ila, Eli Cohen, ya ce hare-haren da Isra’ila ta kai kan wuraren ajiyar mai na Iran manuniya ce kan yadda rikicin da ke gudana ya yi tsanani, kuma “za mu ga ƙarin hare-hare a kwanakin nan,” in ji shi.
Cohen ya bayyana haka ne a wata hira da gidan rediyon Isra’ila Radio 103.
Ya ce sun tsara dukkanin abubuwan da za su taimaka musu wajen illata gwamnatin Iran ta yanzu.
Da aka tambaye ministan game da tsawon lokacin rikicin, sai ya ce “mun san lokacin da muke sa ran cimma duk manufofin da muka sa a gaba. Akwai shiri kan wannan yaƙin, ana samun ci gaba a filin daga, ba ma son mu shiga yanayin da zai sa mu sake dawowa fagen daga nan da shekara ɗaya ko biyu.”