Isra’ila ta yi asarar dala 57 a tattalin arzikinta cikin shekara biyu kan kisan kare dangin Gaza bisa ga alƙaluman da babban bankin kasar ya fitar.
A cikin rahoton shekara-shekara na babban bankin, ya nuna cewa Isra’ila ta yi asarar sehekl biliyan 177, wanda ya yi daidai da dala biliyan 57, tsakanin shekarar 2023 zuwa shekarar 2025.
Bloomberg ta ce yawancin asarar da Isra’ilar tayi yana da alaqa da kisan kiyashin da take yi a Gaza da kuma harin da ta kai Lebanon.
Kazalika rahoton bai haɗa da tasirin da yaƙin da ake gwabza wa tsakanin Isara’ila da Iran ba a yanzu, wanda tuni ya shiga mako na huɗu da fara wa.
A farkon wannan watan, majalisar zartarwar yaƙi ta Isra’ila ta amince a sabunta kasafin kuɗi na ƙasar na shekarar 2026, inda ta ƙara dala biliyan 13 kari kan kasafin kuɗin yaƙinta.
Rahoton ya kuma nuna sauyi a yanayin cinikayya, inda Isra’ila ta fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen Tarayyar Turai takwas.