Sojojin Isra’ila sun ce sun kashe wasu manyan jami’an leƙen asirin Iran biyu, a wasu hare-hare da suke ci gaba da kai wa Iran.
Wata sanarwa da sojojin suka fitar ranar Litinin, ta ce waɗanda aka kashen sun haɗa da Sayed Yahya Hamidi da Jalal Pour Hussein.
Sanarwar ta ce Hamidi ya kasance mataimakin ministan leƙen asiri ne kan harkoki da suka shafi Isra’ila, inda suka ce ya “jagoranci kai hare-hare kan Yahudawa da masu adawa da Iran a ciki da wajen ƙasar”.
Yayin da Hossein kuma ya kasance shugaban sashen leƙen asiri a ma’aikatar leƙen asiri ta Iran.
“An kuma hallaka wasu manyan jami’ai ba ya ga waɗannan biyu,” in ji Isra’ila.