Rundunar sojin Isra’ila ta ce Iran ta harba mata sama da makamai masu linzami 400 tun farkon yaƙin da ta kaddamar a Tehran tare da hadin gwiwar Amurka.
Sai dai ta ce ta kakkabe kusan kashi 92 cikin 100 na makaman da Iran din ta harba.
“Iran ta harba sama da makami 400 masu linzami. Mun samu nasarar kakkabo yawancin su.
Kusan kashi 92 cikin 100 na makaman an kakkabe su,” in ji kakakin rundunar sojin Isra’ila, Lieutenant Colonel Nadav Shoshani.
Makaman Iran sun afka garuruwa biyu a kudancin Isra’ila a ranar Asabar, inda mutane kusan 180 suka jikkata.