Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

‘ISWAP na shirin kai farmaki Borno’

Dakarun sojojin Najeriya a fagen daga a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya

Wani malami da ake dangantawa da ƙungiyar ISWAP ya yi barazanar kai hari a garin Malam Fatori da ke jihar Borno, bayan da sojojin Najeriya suka kashe kusan ‘yan ta’adda 75 a wani artabu da suka yi da su.

Rahotanni sun ce barazanar ta zo ne bayan asarar da ƙungiyar ta yi, inda malamin ya bayyana cewa za su ɗauki fansa kan sojoji da yankin baki ɗaya.

Sai dai jami’an tsaro sun ce sun ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin, tare da tabbatar da cewa suna cikin shiri domin dakile duk wani yunƙurin hari.

Garin Malam Fatori na daga cikin wuraren da sojoji ke ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda a yankin arewa maso gabas.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use